Aljeriya: Wani Tsohon Janar Zai Kalubalanci Shugaba Buteflka A Zaben Shubaban Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34876-aljeriya_wani_tsohon_janar_zai_kalubalanci_shugaba_buteflka_a_zaben_shubaban_kasa
Kwana daya daga sanar da lokacin da za a gudanar da manyan zabukan kasar Aljeriya, Janar Ali Gudairi mai ritaya ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar
(last modified 2019-01-20T03:17:04+00:00 )
Jan 20, 2019 03:17 UTC
  • Aljeriya: Wani Tsohon Janar Zai Kalubalanci Shugaba Buteflka A Zaben Shubaban Kasa

Kwana daya daga sanar da lokacin da za a gudanar da manyan zabukan kasar Aljeriya, Janar Ali Gudairi mai ritaya ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar

Janar Ali Gudairi mai ritaya ya kira yi al'ummar kasar da su goya masa baya domin fitar da kasar daga cikin mawuyacin halin da take ciki.

Gudairi ya kara da cewa; A halin yanzu matasan kasar suna fama da rashin tabbas, da kuma rushewar tsarin da yake tafiyar da gwamnatin kasar, haka nan kuma yaduwar cin hanci da rashawa.

Tsohon janar din na Aljeriya mai shekaru 42 ya yi alkawalin kawo sauyi a cikin kasar idan aka zabe shi.

Wani dan takarar shugabancin kasar shi ne Abu Jarrah Sultani wanda shi ne tsohon shugaban jam'iyyar al'umma da zaman lafiya ta masu kishin addini.

Za a gudanar da zaben shugaban kasar ta Aljeriya ne a  ranar 18 ga  watan Febrairu mai kamawa