DR Congo : Kotun Tsarin Mulki Ta Ce Tshisekedi Ne Ya Ci Zabe
Kotun tsarin mulkin a Jamhuriya DR Congo ta sanar da amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar da hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta sanar a ranar 10 ga wata, wanda ya ayyana dan takarar jam'iyyar adawa Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben.
A sanarwar data fitar a cikin daren jiya kotun, ta kuma yi watsi da dukkan korafe korafen da dan takaran adawan da ya zo na biyu, Martin Fayulu ya shigar a gabanta, wanda suka hada da neman a soke sakamakon zaben.
Kotun ta ce korafen korafen da dan takaran Fayulu ya shigar basu da tushe, kuma bai gabatar da kwararen hujjoji ba.
Tuni dai dan takaran Fayulu, ya yi watsi da hukuncin kotun tsarin mulkin kasar, yana mai sake nanata ayyana kansa a matsayin halataccen zababen shugaban kasar.
Sakamakon zaben wanda aka gudanar a ranar 30 ga watan Disamban bara, da hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da kwarya-kwaryarsa, ya nuna cewa dan takara Felix Tshisekedi ya samu kashi 38 cikin dari, yayin da Martin Fayulu shi na dan takara adawa ya samu kashi 35 cikin dari, sai kuma dan takara dake samun goyan bayan shugaba Kabila, wanda ya zo a matsayi na uku.