Mali : An Kai Hari Kan Tawagar Sojojin MINUSMA
Jan 20, 2019 07:31 UTC
Majiyoyin tsaro daga Mali na cewa an kai wani hari kan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, ta MINUSMA a kasar Mali, wanda kuma ya yi sanadin mutuwar sojoji a kalla guda biyar.
An dai harin ne da sanyin safiyar yau Lahadi, a yankin a Aguelhok, dake arewacin kasar ta Mali a cewar majiyoyin.
Bayannan sun nuna cewa sojojin da suka rasa rayukansu a harin 'yan asalin kasar Chadi ne.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake kai hari kan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, ta MINUSMA a kasar Mali ba.