Gwamnatin Kasar Masar Ta Bukaci A Kwace Dukiyoyin Dan Tsohon Shugaban Kasar.
Gwamnatin kasar Masar ta bukaci a kwace dukiyar dan tsohon shugaban kasar Husne Mubarak da ke kasar Cyprus.
Jaridar Asharqul ausat ta bayyana a shafin labaranta na yau Lahadi kna cewa babban mai gabatar da kara na gwamnatin kasar ya bukaci gwamnatin kasar ta kwace dukiyoyin da Jamal Mubarak ya mallaka a kasar Cyprus..
Mai gabatar da kasar ya kara da cewa Jamal Mubarak da dan'uwansa Ala Mubarak da kuma wasu abokanansu suna samun kazamar riba a kasuwar hannayen jari na kasar ta hanyar da bata dace ba.
Kotun hukunta manya-manyan laifuffuka wacce ta saurari bukatar mai gabatar da kara na gwamnatin kasar ta Masar, ta daje sauraron kasar har zuwa ranar 23 ga watan jeneru da muke ciki.
Mutanen da ake tuhuma a wannan karar dai sun hada da yayan tsohon shugaban kasar su biyu, Jamal da Ala Mubarak, da kuma wasu mutane 07.