Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati A Kasar Sudan.
Mutanen kasar Sudan sun ci gaba da zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaba Umar Hassan Al-bashar kan tsadar rayuwa.
kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa , mutanen kasar sudan sun fito zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaban Umar Hassan Albashir a jiya Talata a garuruwa da dama a kasar daga ciki har da birnin Khartum babban birnin kasar.
Masu zanga zangar suna rera taken bama son Albashir a fadar shugaban kasa. Ammma jami'an tsaron kasar sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga zangar.
Tun ranar 19 ga watan Decemban da ta gabara ce mutanen kasar Sidan suka fara zanga-zangar kin jinan gwamnatin shugaba Umar hassan albashir saboda tsadar rayuwa a kasar,