DR. Congo : Ranar Alhamis, Za'a Rantsar Da Tshisekedi
Jan 23, 2019 07:18 UTC
Majiyoyi daga bangaren gwamnatin DR Congo da makusantan zababen shugaban kasar, Félix Tshisekedi, sun tabbatar da cewa a gobe Alhamis ne za'a rantsar da sabon shugaban kasar.
Mista Tshisekedi, zai maye gurbin shugaba Joseph Kabila, a bikin da za'a gudanar a fadar shugaban kasar.
Wannan dai kusan shi ne karo na farko da wani shugaban kasa zai mika mulki cikin ruwan sanyi a wannan kasa ta D.R Congo, tun bayan sanar da samun yancin kai na kasar a 1960.
Mista, Tshisekedi mai shekaru 55 na shirin zama shugaban kasar na biyar, inda zai gaji shugaba Kabila wanda ke shugabancin kasar tun shekara 2001, bayan ya gaji mulki daga mahaifisa Laurent-Désiré Kabila wanda aka kashe a lokacin.