Wasu Bama-bamai Sun Fashe A Babban Birnin Kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34926-wasu_bama_bamai_sun_fashe_a_babban_birnin_kasar_somaliya
Rahotanni daga kasar Somaliya sun ce a jiya Laraba ne wasu bama-bamai masu karfi su ka tashi a babban birnin kasar Magadishu
(last modified 2019-01-24T08:49:43+00:00 )
Jan 24, 2019 08:49 UTC
  • Wasu Bama-bamai Sun Fashe A Babban Birnin Kasar Somaliya

Rahotanni daga kasar Somaliya sun ce a jiya Laraba ne wasu bama-bamai masu karfi su ka tashi a babban birnin kasar Magadishu

Kafafen watsa labaran kasar ta Somaliya sun ce an girke  motocin biyu masu dauke da bama-baman ne a kusa da wani Banki.

Kungiyar al-Shabab mai alaka da al'ka'ida ta dauki alhakin kai harin.Kungiyar ta riya cewa ta kashe sojojin kasar ta Somaliya 6 a sanadiyyar harin

Tun a cikin 2007 ne kungiyar ta al-Shabab ta fara kai hare-hare a cikin kasar ta Somaliya da zummar kifar da gwamnati. Sai dai rundunar tarayyar Afirka ta yi nasarar korar kungiyar daga cikin yankuna da dama da ta shimfida ikonta a cikinsu da su ka hada da babban birnin kasar Magadishu

Amma har yanzu da akwai wasu kauyuka da suke a karkashin ikon kungiyar.