An Kashe Sojojin Tabbatar Da Zaman Lafiya Biyu A Kasar Mali
Majiyar majalisar dinkin duniya ta bada sanarwan kisan dakarun tabbatar da zaman lafiya na majalisar guda biyu a arewacin kasar Mali
Shafin yanar gizo na "Annshar" na majalisar dinkin duniya ya bayyana a yau jumma'a kan cewa an kashe sojojin Majalisar 2 sannan aka raunata wasu biyu a lokacinda motarsu ta taka nakiya a gefen titin da suke wucewa a wani wuri a kasar ta Mali.
Sau da dama sojojin majalisar sukan mutu sanadiyar tashin boma-boman a kan titunan da suke bi a wasu garuruwa a arewacin kasar ta Mali.
Kasar Mali ta fada cikin tashe -tashen hankula ne tun shekara ta 2012 a lokacinda sojoji suka yi juyin mulki a kasar, amma kuma suka bawa buzaye daga arewacin kasar damar shelanta kafuwar kasar AZAWAD. Sai kuma ba'a dadeba yan ta'adda suka kwace iko da yankin.
Sojojin kasar Faransa ma, sun shigo kasar ta Mali tun tsakiyar shekara ta 2013, amma tare da yawan sojojin kasashen waje a kasar ta Mali sun kasa tabbatar da zaman lafiya a kasar.
Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa akalla fararen hula 500 ne aka kashe a hare-hare daban-daban a kasar ta Mali a shekara ta 2018 da ta shude.