Rufe Ayyukan Gwamnati A Amurka Ya Jawo Mata Asarar Dala Biliyan 6
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34952-rufe_ayyukan_gwamnati_a_amurka_ya_jawo_mata_asarar_dala_biliyan_6
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato wata cibiyar nazari da bincike ta Amurkan na cewa; Rufe wani sashe na ofisoshin gwamnati da aka yi ya ja wa kasar asarar abinda bai gaza dala biliyan 6 ba
(last modified 2019-01-26T04:07:45+00:00 )
Jan 26, 2019 04:07 UTC
  • Rufe Ayyukan Gwamnati A Amurka Ya Jawo Mata Asarar Dala Biliyan 6

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato wata cibiyar nazari da bincike ta Amurkan na cewa; Rufe wani sashe na ofisoshin gwamnati da aka yi ya ja wa kasar asarar abinda bai gaza dala biliyan 6 ba

Cibiyar S&P Global Ratings; ta ce an yi wannan asarar ne a cikin kwanaki 35 na rufe wani sashe na aikin gwamnati wanda ya zo karshe a jiya Juma'a.

Sabani dai ya kunno kai ne a tsakanin shugaban kasa Donald Trump da majalisar kasar, akan gina katangar karfe akan iyakar Amurka da kasar Mexico. Shugaban na kasar Amurka yana son Majalisa ta amince masa da ya kashe dala biliyan biyar da miliyan 700 domin gina katangar

Tun a ranar 22 ga watan Disamba ne aka rufe aiki a wasu ofisoshin gwamnatin kasar ta Amurka.

An kawo karshen lamarin ne bayan da a jiya Juma'a aka cimma yarjejeniyar wucin gadi a tsakanin shugaban kasar da kuma 'Yan Majalisar kasar.