MDD Ta Nuna Damuwarta Kan Yaduwar Cutar Ebola A Kudancin Congo
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana damuwarta a game da yaduwar cutar ebola a kudancin jamhoriyar Dimokaradiyar Congo.
Cikin wani bayyani da ta fitar jiya Assabar, hukumar lafiya ta Duniya ta bayyana cewa yadda cutar ebola ke yaduwa a lardin kudancin jamhoriyar Dimokaradiyar Congo, lamari ne dake barazana ga harakokin tsaron yankin.
Hukumar Lafiyar ta Duniya ta ce sabon binciken da aka gudanar ya nuna cewa adadin mutanan da cutar ebola ta hallaka a kasar Congo ya haura zuwa 439.
Hukumar ta ce matukar ana so a yaki cutar ebola to dole ne duk mutanan da ake da shakku kansu game da kamuwar cutar, a kwantar da su a asibiti, a binciki lafiyarsu, kuma halin da kudancin jamhoriyar Dimokaradiyar Congon ke ciki a yanzu, akwai matsaloli masu yawa na karancin magani.
Tun a watan Mayun shekarar da ya gabata ne cutar Ebolar ta sake billa a garin Bikoro na jahar Équateur dake arewa maso yammacin kasar ta Congo sannan ta wanzu zuwa garin Mbandaka na tsakiyar jahar kafin daga bisa ta sake wanzuwa zuwa yankunan gabashin kasar ta Congo.
Daga shekarar 2014 zuwa yanzu cutar ta Ebola ta billa har so uku a kasar Demokaradiyar ta Congo.
Daga shekarar 2013 zuwa 2016, cutar ta ebola ta salwanta rayukan mutane kimanin dubu 11 a wasu kasashe na yammacin Afirka.