Sudan : Al'Bashir Na Ziyara A Masar
Shugaba Umar Hassan El'Bashir, na Sudan, ya fara wata ziyara a birnin Alkahira na kasar Masar, wadda ita ce ziyararsa ta biyu a ketare, tun bayan soma zanga zangar tsadar rayuwa a kasarsa.
Bayanai da fadar shugaban kasar Masar ta fitar, sun ce da yammacin yau, shuwagannin kasashen biyu zasu gudanar da wani taron manema labarai.
Shugaba El'Bashir wanda ke fuskanatar boren jama'ar kasarsa tun ranar 19 ga watan Disamba, na bukatar samun goyan bayan kawayen kasarsa a yankin da suka hada da Masar din, Saudiyya da kuma Qatar.
Bayan tabarbarewar huldar dake tsakanin kasashen biyu a 2017, lokacin da El Bashir, ya zargi Masar da goyan bayan jagoran 'yan adawa na kasar, bagarorin biyu sun samu magance sabanin dake tsakaninsu, inda a watan Oktoba Sudan ta dage haramcin odar kayayaki daga Masar wanda ta yi na tsawan watanni 17.