Masar: An Kashe Kwamandojin 'Yan Ta'adda Biyu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34980-masar_an_kashe_kwamandojin_'yan_ta'adda_biyu
Majiyar sojan Masar ta ce an kashe manyan kwamandojin 'yan 'ta'adda biyu ne a yankin Sina
(last modified 2019-01-28T04:12:06+00:00 )
Jan 28, 2019 04:12 UTC
  • Masar: An Kashe Kwamandojin 'Yan Ta'adda Biyu

Majiyar sojan Masar ta ce an kashe manyan kwamandojin 'yan 'ta'adda biyu ne a yankin Sina

Kamfanin dillancin Labarun Anatoli na Turkiya ya ambato kakakin sojojin Masar, Tamir al-Rufa'i' yana cewa; baya ga kwamandojin biyu, an kuma kashe wasu tarin 'yan ta'addar masu yawa

A yankin Sina da akwai kungiyoyin 'yan ta'adda da su ka kunshi Ansaru Baitul-Mukaddas da reshe ne na Da'esh, ko Isis. Kungiyar ta 'yan ta'addar sun sha kai hare-hare a cikin sassa daban-daban na kasar Masar

Yankin Sina ta Arewa a kasar Masar yana a matsayin tunga ta kungiyoyi daban-daban na 'yan ta'adda. "Yan ta'addar sun kashe sojoji masu yawa da kuma kai wa majami'u hare-hare.