'Yan Jaridar Masar Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Boren Mutanen Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34981-'yan_jaridar_masar_sun_nuna_goyon_bayansu_ga_boren_mutanen_sudan
Kungiyar 'yan jarida da manazartan kasar Masar sun fitar da sanarwa da a ciki su ka nuna goyon bayansu ga Zanga-zangar neman kawo sauyi da al'ummar Sudan suke yi
(last modified 2019-01-28T04:13:52+00:00 )
Jan 28, 2019 04:13 UTC
  • 'Yan Jaridar Masar Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Boren Mutanen Sudan

Kungiyar 'yan jarida da manazartan kasar Masar sun fitar da sanarwa da a ciki su ka nuna goyon bayansu ga Zanga-zangar neman kawo sauyi da al'ummar Sudan suke yi

Sanarwar ta kunshi yin kira ga gwamnatin shugaba Umar Hassan al-Bashir da ta dakatar da amfani da karfi akan masu Zanga-zangar da kuma sakin dukkanin fursunoni siyasa da ake daure da su

Umar Hassan al-Bashir shugaban kasar Sudan ya ziyarci kasar Masar a jiya Lahadi

Tun a ranar 19 ga watan Disamba na 2018 ne al'ummar Sudan su ka fara gudanar da Zanga-zangar kin amincewa da hauhawar farashin kayan masarufi. Sai dai daga baya ta juye zuwa yin kira ga shugaba Umar Hassan Umar al-Bashir da ya yi murabus daga kan mukaminsa

Majiyar gwamnatin kasar ta Sudan ta ce mutane 19 ne su ka rasa rayukansu a tsawon makwannin na Zanga-zangar. Sai dai majiyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama na cikin gida da kuma waje, sun ce fiye da mutane 40 jami'an tsaron kasar Sudan din su ka kashe.