Kungiyar "Yan Uwa Musulmi" A Masar Ta Bukaci Hadinkan Jam'iyyun Adawa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34986-kungiyar_yan_uwa_musulmi_a_masar_ta_bukaci_hadinkan_jam'iyyun_adawa
Kungiyar "yan uwa musulmi" a kasar Masar ta bukaci jam'iyyun adawa da gwamnatin shugaba Abdulfattah Assisi su dulkule waje guda don tunkararasa.
(last modified 2019-01-28T08:29:42+00:00 )
Jan 28, 2019 08:29 UTC
  • Kungiyar

Kungiyar "yan uwa musulmi" a kasar Masar ta bukaci jam'iyyun adawa da gwamnatin shugaba Abdulfattah Assisi su dulkule waje guda don tunkararasa.

Tashar talabijin ta "Aljazeera" ta kasar Qatar ta nakalto wani bayanin da yayan kungiyar suka fitar a jiya Lahadi, a dai dai lokacinda ake cika shekaru 8 da juyin mulkin watan Yulin shekara ta 2011, wanda yake buakatar dukkan jam'iyyun adawa da gwamnatin shugaba Sisi da suke kasashen waje su dunkule su kafa kungiya guda don tunkararsa daga wajen kasar.

Manufar wannan dunkulewar, inji bayanin ita ce kubutar da mutanen kasar Masar daga takurawar sojojin kasar da kuma maida iko ga hannun mutane, sannnan kubutar da dubban fursinonin siyasa wadandan suke daure a gidajen yakar kasar. 

Tun bayan juyin mulkinn da sojoji suka yi wa zabebben gwamnatin Muhammad Mursi a shekara ta 2011 dai, sojojin da suka kwace mulki suka haramta kungiyar ta Yan uwa musulmi sannan suka tsare shuwagabannin kungiyar daga ciki har da shi tsohon shugaban kasar Muhammad Mursi.