Al'ummar Afirka Ta Tsakiya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Jinin Faransa
Mazauna Bangui babban birnin jamhoriyar Afirka ta Tsakiya sun gudanar da zangar-Zangar adawa da takunkumin sayan makamai da MDD ta kakabawa kasar, tare da dora alhakin hakan a kan kasar Faransa.
Kimanin mutane dubu uku ne ciki har da Piraministan kasar Mathieu Simplice Sarandji suka gudanar da wannan zanga-zanga a yau Litinin tare da neman Majalisar Dinkin Duniya ta dage wa kasar takunkumin da ta kakaba mata na hanata sayan makamai.
A yayin da yake gabatar da jawabi a gaban mahalarta zanga-zangar, Piraministan kasar Afirka ta tsakiyan ya ce takunkumin hana sayan makamai da MDD ta kakabawa gwamnatin kasar ya raunana karfin jami'an tsaron kasar, kuma kamata ya yi Duniya tayi la'akari da halin da kasar take ci, ta dage mata wannan takunkumi.
Mathieu Simplice Sarandji ya kara da cewa gwamnati, na mutunta takunkumin da MDD ta kakabawa kasar, to amma kungiyoyin dake dauke da makamai har yanzu suna samun makamai daga wani hanyoyi mabambanta, wannan doka ce da babu yadda za a yi Al'ummar jamhoriyar Afirka ta tsakiya su amince da ita.
Tun a shekarar 2013 ne, Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa jamhoriyar Afirka ta tsakiya takunkumin saya da sayarwar makamai da kayan yaki.
Wannan dai ba shi ba ne karon farko da mahukuntar birnin Bangui ke neman MDD ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar, to amma har yanzu Majalisar ta ki amincewar da bukatar.
Da dama dai daga mahalarta zanga-zangar na ganin cewa wakilin kasar Faransa na kwamitin tsaron MDD ne ya hana dagewa kasar Takunkumi.
Kamar ko wata shekara a wannan alhamis ne kwamitin tsaron MDD zai yi zama na jadadda ko dage takunkumin saya da sayarwar makamai da kayan yaki da ta kakabawa jamhoriyar Afirka ta tsakiya.