Amurka Ta Kakaba Wa Kamfanin Man Fetur Na Kasar Venezuela Takunkumi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34994-amurka_ta_kakaba_wa_kamfanin_man_fetur_na_kasar_venezuela_takunkumi
A daren Jiya Litinin ne gwamnatin Amurka ta sanar da kakaba wa kamfanin man fetur din kasar Venezuela takunkumi
(last modified 2019-01-29T04:18:47+00:00 )
Jan 29, 2019 04:18 UTC
  • Amurka Ta Kakaba Wa Kamfanin Man Fetur Na Kasar Venezuela Takunkumi

A daren Jiya Litinin ne gwamnatin Amurka ta sanar da kakaba wa kamfanin man fetur din kasar Venezuela takunkumi

Mai bai wa fadar White House shawara akan harkokin tsaron kasa, John Bolton da kuma shugaban Baitul-Malin Amurka  Stephen Menochen suka fitar da sanarwa ta hadin gwiwa akan sabon takunkumin.

Bugu da kari sabon takunkumin ya kunshi rike kudaden da kamfanin man fetur din Venezuela yake da su a Bankunan Amurka da su ka kai dala biliyan 7

Manufar sabon takunkumin kamar yadda mahukuntan na Amurka su ka ambata shi ne yanke duk wata hanya ta samun kudaden shiga ga shugaba Nicolas Maduro da kuma mika kudaden ga Juan Guaido wanda ya nada kansa a matsayin shugaban kasa

Tun daga makon da ya gabata ne dai gwamnatin Amurka ta kara kaimi a matsin lambar da take yi wa halartacciyar gwamnatin Venezuela domin durkusar da ita

A ranar Larabar da ta gabata ne dai shugaban Majalisar dokokin kasar Venezuela kuma jagoran yan hamayya Juan Guaido ya shelanta a matsayin shugaban kasa.

Kasar Amurka da kawayenta sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Guaido tare da yin kira ga jami'an tsaron kasar da su bijire wa shugaba Nicolas Muduro.

Su kuwa kasashen Iran, Rasha, China, Cuba, Afirka Ta Kudu, sun nuna cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Nocolas Maduro.