Mutanen Kasar Afirka Ta Tsakiya Sun Yi Zanga-zanga Akan Kasar Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34995-mutanen_kasar_afirka_ta_tsakiya_sun_yi_zanga_zanga_akan_kasar_faransa
Mazauna birnin Bongui sun fito kan tituna suna masu nuna kin yarda da takunkumin hana sayen makamai da MDD ta kakaba wa kasarsu, suna masu zargin Faransa da laifi
(last modified 2019-01-29T04:22:58+00:00 )
Jan 29, 2019 04:22 UTC
  • Mutanen Kasar Afirka Ta Tsakiya Sun Yi Zanga-zanga Akan Kasar Faransa

Mazauna birnin Bongui sun fito kan tituna suna masu nuna kin yarda da takunkumin hana sayen makamai da MDD ta kakaba wa kasarsu, suna masu zargin Faransa da laifi

Mutanen da adadinsu ya kai 3000 tare da Pira Ministan kasar  Mathieu Simplice Sarandji sun bukaci ganin Majalisar Dinkin Duniya ta dauke takunkumin da ta kakaba wa kasarsu

Pira Minista  Mathieu Simplice Sarandji da ya gabatar da jawabi a wurin Zanga-zangar ya bayyana cewa; "Takunkumin da aka kakaba wa kasar ya raunana karfinta ta fuskar tsaro, don haka ya zama wajibi a dage shi."

Mathieu Simplice Sarandji ya kara da cewa; Gwamnati tana aiki da yarjejeniyar,amma kungiyoyin da suke dauke da makamai suna samun karin makamai ta hanyoyi daban-daban

Tun a 2013 ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa Afirka Ta Tsakiya takunkumin hana mata sayen makamai.

shugabannin kasar ta Afirka Ta Tsakiya sun sha yin kira ga Majalisar Dinkin Duniyar da ta kawo karshen takunkumin.

Da dama daga cikin masu Zanga-zangar sun dora alhakin kakaba wa kasarsu takunkumi akan kasar Faransa wacce take da kujerar din-din-din a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya

A jibi alhamis ne ake sa rana cewa kasar Faransa da sauran mambobin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya za su dauki mataki akan kara wa'adin takunkumin zuwa wata shekara guda