Gwamnatin Sudan Ta Sallami Dukkan Masu Zanga Zanga Da Ake Tsare Da
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35003-gwamnatin_sudan_ta_sallami_dukkan_masu_zanga_zanga_da_ake_tsare_da
Gwamnatin Sudan ta sanar da sallamar dukkan mutanen da ake tsare da tun bayan soma zanga zangar tsadar rayuwa a kasar a cikin watan Disamban bara.
(last modified 2019-01-29T13:13:32+00:00 )
Jan 29, 2019 13:13 UTC
  • Gwamnatin Sudan Ta Sallami Dukkan Masu Zanga Zanga Da Ake Tsare Da

Gwamnatin Sudan ta sanar da sallamar dukkan mutanen da ake tsare da tun bayan soma zanga zangar tsadar rayuwa a kasar a cikin watan Disamban bara.

Wata sanarwa da ma'aikatar sadarwa ta klasar ta fitar a yau, ta ce shugaban hukumar leken asiri na kasar ya bada umarnin a saki dukkan mutanen da ake cafke a yayin zanga zangar da ake kan shugaban kasar Umar Al'bashir.

A cewar kungiyoyin kare hakkin bil adama, sama da mutum 1, 000 ne da suka hada da masu zanga zanga da jiga jigan 'yan adawa da masu fafatuka da kuma 'yan jarida aka cafek tun bayan boren da jama'ar kasar ta Sudan suka soma a ranar 19 ga watan Disamba na shekara 2018 data gabata a fadin kasar domin kalubalantar matakan gwamnatin kasar na kara farashin kayan masarufi.

Zanga zangar da daga bisani ta rikide zuwa ta kyammar gwamnatin shugaba El' Bashir, wanda ke mulkin kasar yau kusan shekaru 30, bayan wani juyin mulki a cikin shekara 1989.

Alkalumman da hukumomin kasar suka fitar sun nuna cewa mutum 30 ne suka mutu tun soma zanga zangar, saidai a cewar wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama mutane akalla 40 ne suka mutu a boren, a yayin da bangaren 'yan adawa na kasar ke cewa mutanen da suka rasun ya kai 50.