Mali: An Kashe Sojojin Gwamnati Biyu
Ma'aikatar tsaron kasar Mali ta bayyana cewa; An kashe sojojin biyu ne a wani hari da aka kai musu a kudancin kasar, tare kuma da jikkata wasu 10
Kamfanin dillancin labarin faransa daga birnin Bamako ya ambato cewa; An kashe maharan da su ka kai wa sansanin sojan kasar a yankin Gao hari
A wani rahoto na watanni uku-uku da Majalisar Dinkin Duniya take fitarwa ta bayyana cewa; Fiye da rabin hare-haren da aka kai wa sojojin Mali, an kai su ne a cikin tsakiyar kasar da kuma arewacinta.
Kasar Mali ta fada cikin matsalar tsaro tun a cikin shekarar 2012.
Kasar Faransa wacce ta yi wa Mali mulkin mallaka ta aike da sojoji a kasar tun a 2013 domin fada da kungiyoyin da suke dauke da makamai masu fada da gwamnatin kasar
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoto da a ciki ta bayyana cewa; A 2018 kadai rikice-rikicen kasar sun ci rayukan fararen hula 500