Afrika Ta Tsakiya : An Cimma Yarjejeniya Zaman Lafiya A Sudan
Gwamnatin Jamhuriya Afrika ta tsakiya, ta sanar da cimma yarjejeniyar zaman lafiya, tsakaninta da gungun kungiyoyi masu dauke da makamai.
An dai cimma wannan yarjejeniyar ce a birnin Khartoum na kasar Sudan, kamar yadda gwamnatin kasar ta sanar a shaffinta na Twitter.
Sanarwar ta kara da cewa a gobe Lahadi ne bangarorin zasu kammala daddale yarjejeniyar , sannan a rattaba mata hannu a kwanaki masu zuwa a Bangui babban birnin kasar.
Shi ma da yake tabbatar da hakan, kwamishinan kwamitin kungiyar tarayya Afrika, kan zaman lafiya da tsaro, Smaïl Chergui, ya ce an cimma matsaya kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Bangui da kuma wakilan gungun masu dauke da makamai 14 a birnin Khartoum, kuma a cewarsa yanzu haka suna kan aiki na ganin dukkan bangarorin sun amince da abinda yarjejeniyar ta kunsa, ciki har da batun afuwa wa jagororin gungun masu dauke da makamai da ake takaddama a akai.
Tattaunawar zaman lafiya da aka fara a ranar 25 ga watan Janairu da ya gabata, an dakatar da ita a ranar Alhamis data gabata, saboda rashin fahimtar juna akan batun na yin afuwa wa jagororin kungiyoyin masu dauke da makamai da gwamnatin kasar ke zargi da aikata muggan laifuka.
Bisa matsin lamba na abokan huldarta na kasashen yamma, gwamnatin Bangui ta ki amince yin afuwa ga jagororin masu dauke da makaman, wadanda da dama daga cikinsu ke fuskantar takunkumi na MDD, ko kuma aka ambato su a cikin jerin sunayen wadanda wasu kungiyoyin kasa da kasa ke zargi da sabawa dokokin kasa da kasa da kuma keta hakkin bil adama.