An Kashe Yan Bindiga 20 A Kasar Congo Demokradiyya.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35065-an_kashe_yan_bindiga_20_a_kasar_congo_demokradiyya.
Rundunar sojojin kasar Demokradiyar Kongo ta bada sanarwan cewa ta kashe yan bindiga 20 a gabancin kasar a wani sumamen da ta kai kan mabuyarsu a yankin.
(last modified 2019-02-03T15:41:50+00:00 )
Feb 03, 2019 15:41 UTC
  • An Kashe Yan Bindiga 20 A  Kasar Congo Demokradiyya.

Rundunar sojojin kasar Demokradiyar Kongo ta bada sanarwan cewa ta kashe yan bindiga 20 a gabancin kasar a wani sumamen da ta kai kan mabuyarsu a yankin.

Kamfanin dillancin labaran Anatoliya ya nakalto majiyar rundunar sojojin kasar na Kongo suna fadar haka a yau Lahadi.

Labarin ya kara da cewa Mayakan yan kungiyar "Patriotic Union for the Liberation of Congo" ko UPLC ne sojojin suka kashe a lokacin sumamen.

Kafin haka dai rundunar ta bayyana cewa mayakan kungiyar sun fara nuna wasu alamu na son tada hankali a yankin. An kafa kungiyar "Patriotic Union for the Liberation of Congo" a shekara ta 2018 da ta gabata, sannan tana cikin daruruwan kungiyoyin yan tawaye da suke tada hankali a gabacin kasar ta Kongo. 

An dau shekaru fiye da 20 rabuwa da samun zaman lafiya a gabancin kasar democradiyyar Kongo.