An Kashe Mutane 6 A Fadar Kabilanci A Kasar Guinea Conakry
Feb 03, 2019 15:43 UTC
Gwamnatin kasar Guinea Conakry ta bada sanarwan cewa mutane 6 ne aka kashe sanadiyyar fadan kabilanci a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Xinhuwa na kasar Cana ya nakalto majiyar gwamnatin kasar ta Guinea Conakry tana fadar haka a yau Lahadi . Ta kuma kara da cewa fadan ta aukune a wani wuri kolimita 800 daga kudu masu gabacin babban birnin kasar Conakry.
Labarin ya kara da cewa kabilu biyu ne suka yi fada a tsakaninsu kan mallakar wani wuri mai arzikin zinari a kasar, mai suna Mandiana.
Kabilun biyu sun dade suna sabani kan mallakar wannan wari mai arzikin zinari kafin fadan na yau Lahadi. Bayan barkewar fadar gwamnatin kasar ta tora jami'an tsaro zuwa garin don dawo da zaman lafiya.