Fadan Kabilanci Ya Ci Rayukan Mutum 6 A Kasar Guine Conakry
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35079-fadan_kabilanci_ya_ci_rayukan_mutum_6_a_kasar_guine_conakry
Gwamnatin kasar Guine Conakry ta sanar da mutuwar mutum 6 sanadiyar fadan kabilanci a kasar.
(last modified 2019-02-04T15:44:50+00:00 )
Feb 04, 2019 15:44 UTC
  • Fadan Kabilanci Ya Ci Rayukan Mutum 6 A Kasar Guine Conakry

Gwamnatin kasar Guine Conakry ta sanar da mutuwar mutum 6 sanadiyar fadan kabilanci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya nakalto hukumomin kasar Guine Conakry na cewa rikicin kabilancin ya auku ne a garin Mandiana mai nisan kilomita 800 dake kudu maso gabashin Conakry babban birin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 6 da kuma jikkata wasu da dama na daban.

Sanarwar ta ce fadar ya auku ne tsakanin mazaune kauyuka biyu na yankin, sanadiyar mallakar wani yanki mai arzikin  Zinari.

A yayin fadan, bangarorin biyu sun yi amfani da sanduna gami da yukake, saidai tun kafin fadan ya yi kamari, hukumomin yankin suka aike da jami'an 'yan sanda domin kwantar da tarzoma.

Sama da shekaru 20 da ake samu rikicin kabilanci a kasar Guine Conakry, daga lokaci zuwa lokaci, lamarin da ya yi sanadiyar salwanta rayukan fararen hula da dama.