An Tsawaita Dokar Ta Baci A Kasar Tunisiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35082-an_tsawaita_dokar_ta_baci_a_kasar_tunisiya
Shugaban kasar Tunisiya ne ya sanar da sake tsawaita wa'adin dokar ta bacin na tsawon wata guda a wata sanarwa da jiya Litinin da dare
(last modified 2019-02-05T04:05:40+00:00 )
Feb 05, 2019 04:05 UTC
  • An Tsawaita Dokar Ta Baci A Kasar Tunisiya

Shugaban kasar Tunisiya ne ya sanar da sake tsawaita wa'adin dokar ta bacin na tsawon wata guda a wata sanarwa da jiya Litinin da dare

Ofishin shugaban kasar Muhammad al-Baji El-Sibsy ya  fada a cikin sanarwar cewa; Daga ranar Talata 5 ga watan Febrairu ne dokar za ta cigaba da aiki har zuwa 6 ga watan Maris na 2019

Ofishin shugaban kasar ya ce an dauki wannan matakin ne baya yin shawara da Pira minista da kuma majalisar dokoki

An fara aiki da dokar ta bacin ne a cikin kasar ta Tunisiya tun a ranar 24 ga watan Nuwamba na 2015 bayan wani harin ta'addanci da aka kai wa motar Safa mai dauke da jami'an tsaron kasar.tare da kashe da dama daga cikinsu