Ana Cigaba Da Zanga-zangar Nuna Kin Jinin Gwamnatin Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35084-ana_cigaba_da_zanga_zangar_nuna_kin_jinin_gwamnatin_sudan
Mutanen kasar Sudan sun ci gaba da gudanar da Zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a garuruwa daban-daban na kasar da suka hada da birnin Khartum
(last modified 2019-02-05T04:09:53+00:00 )
Feb 05, 2019 04:09 UTC
  • Ana Cigaba Da Zanga-zangar Nuna Kin Jinin Gwamnatin Sudan

Mutanen kasar Sudan sun ci gaba da gudanar da Zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a garuruwa daban-daban na kasar da suka hada da birnin Khartum

Rahotanni daga kasar ta Sudan sun ce a jiya Litinin masu Zanga-zangar sun ci gaba da nuna kin amincewarsu akan tsadar rayuwa tare da yin kira ga shugaba Umar al-Bashir da ya sauka daga kan mulki

Jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa masu Zanga-zangar

Kungiyar ma'aikatan kasar Sudan da ta kunshi likitoci, injiniyoyi da malaman jami'oi ce take gayyatar mutane su rika fitowa Zanga-zangar neman shugaban kasa Umar Hassan al-Bashir da ya yi murabus

Tun ranar 19 Disamba na shekarar da ta gabata ne dai aka fara Zanga-zanga a kasar ta Sudan saboda nuna kin yarda da karin kudin burodi da makamashi. 

Majiyar gwamnatin kasar ta ce ya zuwa yanzu an kashe mutane 30, sai dai kungiyoyin kare hakkin bil'adama na cikin gida da waje sun ce adadin wadanda aka kashe sun kai 40.

A cikin shekaru 30 kasar Sudan ba ta taba fuskantar bijirewa gwamnati kamar na wannan lokacin ba.

Gwamnatin Sudan ta kafa dokar ta baci a cikin wasu yankunan kasar domin dakile karfin Zanga-zangar.

Umar Hassan al-Bashir ya hau kan karagar mulkin kasar ne tun a 1993.