Jiragen Yakin Faransa Sun Kai Hari A Kasar Chadi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35087-jiragen_yakin_faransa_sun_kai_hari_a_kasar_chadi
A jiya Litinin ne jiragen yakin kasar Faransa su ka kai hari akan wata kungiya mai dauke da makamai a arewacin kasar Chadi
(last modified 2019-02-05T04:35:40+00:00 )
Feb 05, 2019 04:35 UTC
  • Jiragen Yakin Faransa Sun Kai Hari A Kasar Chadi

A jiya Litinin ne jiragen yakin kasar Faransa su ka kai hari akan wata kungiya mai dauke da makamai a arewacin kasar Chadi

Ma'aikatar harkokin tsaron kasar Faransa ta ce ta kai harin ne akan wata kungiyar masu dauke da makamai na kasar Libya da su ka yi kuste cikin kasar

Bayanin ma'aikatar harkokin tsaron kasar ta Faransa ya ci gaba da cewa; Mutanen suna cikin ayarin motoci ne da su ka kai 40, kuma sa'aoi 48 da su ka gabaci kai harin an san da shigowar su cikin Chadi

Ma'aikatar harkokin tsaron kasar ta Faransa ta kuma ce; An kai harin ne dai bisa bukatar gwmanatin kasar Chadi

Faransa ta dade tana tsoma baki a harkokin cikin gidan nahiyar Afrika da sunan fada da ayyukan ta'addanci.