Dakarun Tsaron Libiya Sun Kwace Rijiyoyin Man Fetir Na Al-Sharara
Kakakin Rundunan tsaron kasar Libiya bisa jagorancin Janar Khalifa Haftar ya sanar da cewa a daren jiya Laraba, dakarun tsaron kasar sun samu nasarar kwace rijiyoyin man fetir na Al-sharara dake a matsayin babbar rijiyan man kasar.
Kamfanin dillancin labaran Fars ya nakalto Ahmad Mismari mai magana da yawun rundunar tsaron kasar Libiya bisa jagorancin janar Khalifa Haftar sun samu nasarar fatattakar 'yan ta'addar daga rijiyar man fetir na Al-sharara a daren jiya laraba, kuma a halin da ake ciki yanzu, Sojojin kasar na gab da shiga garin Murzuk na kudancin kasar domin farautar 'yan ta'adda.
Kasar Libiya dai ta ce fada cikin rikici yaki tun bayan borin da matasan kasar suka yi a shekarar 2011, inda kasar Amurka da Dakarun tsaron Nato suka shiga kasar suka kuma kashe marigayyi kanal Mu'amar Kaddafi.
Sakamakon sabanin dake akwai tsakanin 'yan siyasa, kimanin shekaru 4 da suka gabata, kasar ta kasance tana da Majalisu guda biyu, guda a garin Tabruk dake gabashin kasar, guda guda a Tripoli babban birnin kasar.
Majalisar dake birnin Tabruk na samun goyon bayan sojojin kasar bisa jagorancin Khalifa Haftar, ita kuma gwamnatin hadin kan kasar ta Alwufak dake da matsuguni a Tripoli na samun goyon bayan kasashen Yamma da Amurka.
Kungiyoyin 'yan ta'adda dai sun yi amfani da wannan sabani wajen mamaye rijiyoyin man fetir din kasar.