Mun Kai Hari Chadi Don Murkushe Juyin Mulki Inji Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35190-mun_kai_hari_chadi_don_murkushe_juyin_mulki_inji_faransa
Faransa ta sanar da cewa gungun 'yan tawayen data kai wa hari a kasar Chadi, na shirin yin juyin mulki ne wa gwamnatin shugaba Idriss Deby na Chadi ne.
(last modified 2019-02-12T13:55:28+00:00 )
Feb 12, 2019 13:55 UTC
  • Mun Kai Hari Chadi Don Murkushe Juyin Mulki Inji Faransa

Faransa ta sanar da cewa gungun 'yan tawayen data kai wa hari a kasar Chadi, na shirin yin juyin mulki ne wa gwamnatin shugaba Idriss Deby na Chadi ne.

Da yake sanar da hakan ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Yves Le Drian, ya ce harin da kasarsa t akai a farkon watan nan a arewa maso gabashin Chadi, ta kai shi ne kan gungun 'yan tawaye dake son kifarda gwamnatin shugaba Deby.

Mista le Drian ya kara da cewa, shugaba Deby ne da kansa ya bukaci taimakon Faransa, a cikin wata wasika, domin murkushe 'yan tawayen, da suka fito daga kudancin Libiya mai fama da rikici, domin kifarda gwamnatin Shugaba Deby da karfin bindiga.

Kuma bisa bukatar mahukuntan N'Djamena, ne Faransa ta kai jerin hare hare sama har sau uku kan ayarin motocin gungun 'yan tawayen na UFR.

A don haka ne ma'aikatar harkokin wajen Faransar ta ce hare haren data kai suna tafiya kafada da kafada da dokokin kasa da kasa.

Ko a shekara 2008 ma kasar ta Faransa ta taba murkushe wani yunkurin juyin mulki da 'yan tawayen na UFR suka so yi wa gwamnatin Idriss Deby.

Wata sanarwa da kungiyar 'yan tawayen ta fitar ta bakin kakakinta, ta sha alwashin daukar fansa kan hare haren da ala kai mata da kuma mayakanta da sojojin Chadi suka cafke a baya bayan nan.