An Kama Yan Jarida Da Malaman Jami'a Da Dama A Kasar Sudan.
Wasu labarai daga kasar Sudan sun bayyana cewa an kama yan jarida da kuma malaman jami'o'i a wasu tarorroka da suke gudanarwa a wurare daban-daban a birnin Khartum babban birnin kasar a jiya Talata.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa tarurrukan na nuna goyon baya ga masu adawa da gwamnatin shugaba Umar Hassan Albashir ne, kuma adadin wadanda aka kama sun kai mutane 16.
Tun ranar 19 ga watan Decemban da ya gabata ne mutanen kasar Sudan suka fara zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaba Umar Hassan Albashir, bayan da farashin abinci musamman bredi da kuma sauran bukatun yau da kullum suka yi tashin goron zabi a duk fadin kasar .
Jami'an tsaron kasar Sudan dai sun bayyana cewa mutane kimani 30 suka rasa rayukansu tun lokacinda aka fara boren. Amma kungiyoyin kare hakkin bil'adama na kasa da kasa sun bayyana cewa adadin wadanda aka kashe sun kai mutum 40.
Shugaba Albashir dai ya fara shugabancin kasar Sudan ne a shekara 1993, kuma a halin yanzu yana da damar ci gaba da shugabancin kasar har zuwa shekara ta 2020.