Sudan:An Kame Malaman Jami'o'i Da "Yan Jarida
Jami'an tsaron kasar Sudan sun kame malaman jami'oi da kuma wasu 'yan jarida a jiya Talata
Kamfanin dillancin labarun "Nasim" ya ce; Mutanen da aka kama suna cikin jerin masanan kasar ta Sudan da suke nuna goyon bayansu ga boren da al'ummar kasar da kuma kira ga shugaban kasar Umar Hassan al-Bashir da ya yi murabus
Wasu masu fafutuka a kasar ta Sudan sun nasar a shafukan sada zumunta cewa; Adadin wadanda aka kama din sun kai 16
Al'ummar kasar Sudan ta fara gudanar da Zanga-zanga ne a ranar 19 ga watan Satumba na shekarar 2018 da ta gabata domin nuna kin amincewa hauhawar farashin kayan masarufi. Zangar-zangar ta juye zuwa kira ga shugaban kasar Umar Hassan al-Bashir da ya sauka daga kan mulki
Majiyar gwamnati ta ce ya zuwa yanzu mutane 30 ne aka kashe, yayin da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce; An kashe mutane 40
Wannan dai shi ne bore mafi girma da gwamnatin shugaban Umar Hassan al-Bashir ta fuskanta a cikin shekaru 30 na mulki
Al-Bashir ya zama shugaban kasa ne a 1993, kuma zangonsa na shugabanci zai zo karshe a 2020. Sai dai bisa tsarin mulkin kasar da aka yi wa kwaskwarima zai iya yin tararce har illa masha Allahu