An Kashe Mayakn Kungiyar Al-shabab 12 A Cikin Kasar Somalia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35206-an_kashe_mayakn_kungiyar_al_shabab_12_a_cikin_kasar_somalia
Akalla mayakan kungiyar alshabab 12 ne Amurka ta ce ta kasha a cikin kasar Somalia a jiya.
(last modified 2019-02-14T04:30:11+00:00 )
Feb 14, 2019 04:30 UTC
  • An Kashe Mayakn Kungiyar Al-shabab 12 A Cikin Kasar Somalia

Akalla mayakan kungiyar alshabab 12 ne Amurka ta ce ta kasha a cikin kasar Somalia a jiya.

Tashar talabijin ta Russia today ta bayar da rahoton cewa, dakarun Amurka da ke gabashin nahiyar Afrika sun ce sun kasha mayakan kungiyar Alshabab a cikin kasar Somalia ta hanyar yin amfani da jiragen yaki marassa matuki.

Sojojin na Amurka sun bayyana hare-haren nasu a cikin Somalia da cewa sun gudana cikin nasara, domin kuwa sun rage karfin ‘yan ta’adda.

Tun a cikin shekara ta 2011 ce dai dakarun kasa da kasa suka fara gudanar da ayyukan soji a cikin kasar Somalia da nufin murkushe kungiyar Alshbab wadda take da dangantaka da kungiyar Alkaida.

Amurka tana yin amfani da wannan damar domin kaddamar da hare-hare a cikin kasar Somalia da sunan taimakawa wajen murkushe kungiyar Alshabab.