Gawa Ta Tarwatse Da Likitan Sojoji A Burkina Faso
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35219-gawa_ta_tarwatse_da_likitan_sojoji_a_burkina_faso
A Burkina Faso, wata gawa da aka dana wa bam ta tawatse da wani likitan soji tare da raunata wasu 'yan sanda biyu a yankin Djibo dake arewacin kasar.
(last modified 2019-02-15T00:10:03+00:00 )
Feb 15, 2019 00:10 UTC
  • Gawa Ta Tarwatse Da Likitan Sojoji A Burkina Faso

A Burkina Faso, wata gawa da aka dana wa bam ta tawatse da wani likitan soji tare da raunata wasu 'yan sanda biyu a yankin Djibo dake arewacin kasar.

Majiyoyon tsaro daga yankin sunh shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, jami'in wanda babban soji ne mai matsayin ofisa wanda shi ne likitan bataliyar sojin arewacin kasar , ya ransa a lokacin da bam ya tarwatse da gawar a lokacin da yake gudanar da bincike kan gawar da aka gano kan titi.

Bayannan sun ce gawar ta tarwatse ne lokacin da likitan ya yi kokarin juyata, kuma nan take ne likitan ya rasa ransa, kuma 'yan sanda biyu suka raunana, wanda kuma guda daga cikinsu ya ji munanen raunuka.

Tawagar jami'an tsaron data kunshi sojoji da 'yan sanda ta isa yankin ne bayan da aka sanar da ita cewa an ga wata gawa sanye da kakin soja kan titi.

A 'yan watannin baya bayan nan, kasar Burkina Faso, dake yankin Sahel, na fuskantar kalubale na rashin tsaro dake da nasaba da mayakan dake ikirari da sunan jihadi, ko a 'yan kwanakin da suka gabata ma, wasu jami'an tsaron Jandarma biyar na kasar sun rasa rayukansu a wani hari da ake dangantawa dana mayakan a daidai lokacin da kasar ke karbar bakuncin taron shuwagabannin kungiyar G5-Sahel, data hada kasashen ( Chadi, Nijar, Mali, Maurotania da kuma Burkina fason) wadanda suka runsinar hadin gwiwa ta soji  da yaki da ta'addanci da safara mutane da muggan kwayoyi a yankin.

Alkalumman da kamfanin dilancin labaren AFP, ya fitar sun nuna cewa, tun daga shekara 2015, hare haren mayakan na kungiyar jihadi ta Ansaroul Islam da gungun mayakan islama na (GSIM), sun yi sanadin mutuwar mutane sama da 300 a wannan kasa ta Burkina Faso.