An Kashe Mutane Fiye Da 60 A Jahar Kaduna
Wasu 'yan bindida da ba a san ko su wane ne ba sun kaddamar da hare-hare a kan fararen hula a cikin karamar hukumar Kajuru da ke jahar Kaduna a arewacin Najeriya a jiya Juma'a.
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindigar sun kashe mutane da dama, inda a hukumance ake kaddara adadin da cewa ya kai mutane 66 akasarinsu kuma mata ne da kananan yara, kamar yadda mahukuntan jahar ta Kaduna suka tabbatar.
Hare-haren 'yan bindigar sun fi tsananta ne a wasu rugagen fulani da ke cikin karamar hukumar ta Kajuru, inda suka yi kisan gilla a kan mazauna rugagen.
Mahukuntan jahar Kaduna sun yi Allawadai da harin, tare da kiran shugabanni na gargajiya na yankin gami da malaman addini da su dauki matakai na kwantar da hankalin jama'a, da kuma nisantar duk wasu ayyuka na daukar fansa, kamar yadda kuma mahukuntan jahar suka sha alwashin gudanar da bincike kan lamarin, domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika.