Somalia Na Neman Sulhu A Takkadama Da Kenya
Kasar Somalia na nemi a kai zuciya nesa a takkadamar da ta kunno kai tsakaninta da makobciyarta Kenya, kan yankin nan dake iyakarsu wanda ya kunshi ruwa.
Wannan dai ya biyo bayan da kasar ta Kenya, ta kirayi jakadanta dake Mogadisho domin tuntuba, kan kan yankin na ruwa da suke da sabani a kai.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Somalia, ta fitar a jiya Lahadi ta ce, al'ummar Somalia, da Kenya wadanda ke raba al'adu da tarihi masu karfi, wandanda ba za'a iya katse su ba, sakamakon wani sabani ko rashin fahimta juna tsakaninsu.
A ranar Asabar data gabata ne, gwamnatin Kenya ta sanar da kiran jakadanta a Somalia, don tuntuba, bayan kuma umurtar jakadan na Somalia a Nairobi da ya koma gida, bayan cewa a shirye take ta kare hurimin kasarta ta ko wanne irin hali.
Kenya dai ta ce tana maida martani ne kan matakin gwamnatin Somalia, na sanya wasu cibiyoyi masu arzikin man fetur da iskar gas a yankin na ruwa a kasuwa da kasashen biyu suke takkadama a kai, zargin da gwamnatin Mogadisho ke ci gaba da musuntawa.