Jami'an Tsaron Sudan Sun Kashe Mutum Guda A Zanga-Zanga
Jami'an tsaron kasar Sudan sun kashe mutum guda a zanga-zangar da ake gudanarwa akasar domin yin kira ga shugaba Albashir ya sauka daga kan shugabancin kasar.
Rahotanni daga kasar ta Sudan sun tabbatar da cewa, a daren jiya jami'an 'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da duka da kulake wajen tarwatsa masu gudanatr da zanga-zangar kin jinin gwamnatin Albashir a cikin birnin Khartum fadar mulkin kasar ta Sudan, wanda hakan ya yi sanadiyya mutuwar akalla mutum daya daga cikin masu zanga-zangar da kuma jikkatar wasu da dama.
Jami'an gwamnatin Sudan suna cewa ya zuwa akalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu tun daga lokacin fara zanga-zangar a ranar 19 ga watan Disamban shekarar da ta gabata ya zuwa yanzu, yayin da kungiyoyin farar hula da kuma hukumomi na kasa da kasa suke cewa adadin ya haura hakan.
Jama'a sun fara zanga-zangar ne domin nuna rashin amincewarsu da karin farashin kudin burodi da kuma makamashi, amma daga bisani ta rikide ta koma ta adawa da gwamnatin kasar.