Wani Jirgin Soja Ya Fadi A Kasar Aljeriya
Feb 21, 2019 08:46 UTC
Rahotanni da suke fitowa daga kasar ta Aljeriya sun ce; Jirgin da ya fadi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 2 da suke cikinsa
Jirgin ya fadi ne jiya Laraba da dare a yankin Tiaret da ke arewacin kasar ta Aljeriya
Kawo ya zuwa yanzu babu wani cikakken bayani da ya fito daga ma'aikatar tsaron kasar dangane da musabbabin faduwar jirgin sojan
Ana yawan samun hastarin jiragen sama a kasar Aljeriya a cikin shekarun bayan nan. A watan Aprilu na 2018 ma dai wani jirgin ya fado a kusa da filin saukar jiragen sama na Bufarik tare da kashe dukkanin mazaunansa 257.