Najeriya : Komi Ya Kammala Don Gudanar Da Zabe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35316-najeriya_komi_ya_kammala_don_gudanar_da_zabe
Gwamnahtin tarayyar Najeriya ta bayar da umarnin rufe  kan iyakokin kasar saboda zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dattawa da za a yi a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu 2019.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Feb 22, 2019 01:49 UTC
  • Najeriya : Komi Ya Kammala Don Gudanar Da Zabe

Gwamnahtin tarayyar Najeriya ta bayar da umarnin rufe  kan iyakokin kasar saboda zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dattawa da za a yi a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu 2019.

A wata sanarwa da Kwantirola Janar na Hukumar shige da fice ta Najeriya Mohammad Babandede, ya fitar a yau Alhamis, kamar yadda Ministan kula da harkokin cikin gida na Najeriya Abdurahman Bello Dambazau ya bayar da umarni.

Dokar za ta soma aiki ne tun daga karfe 12 na ranar Juma’a 22 ga Fabrairu 2019 zuwa karfe 12 na ranar Lahadi 24 ga Fabrairu 2019.

Sanarwar ta ce, an dauki matakinne saboda a tabbatar da an yi zabe cikin lumana a fadin kasar.

Haka zalika kuma gwamnatin aksar ta sanar da ranar yau Juma'a a matsayin hutu domin baiwa al'ummar kasar damar shirya kada kuri'a a zaben na gobe idan Allah ya kai.

Jiye ne dai aka kawo karshen yakin neman zaben inda Sama da 'yan Najeriya miliyan 84 ne zasu kada kuri'a a zaben na gobe da ya hada dana shugaban kasa, 'yan majalisar datijai dana dokoki.

A ranar Asabar data gabata ne hukumar INEC ta sanar da dage zaben saboda matsalolin isar kayan aiki a wasu sassan kasar, amma yanzu hukumar ta ce komi ya kammala kuma za'a je zaben a gobe.