Amurka Ta Kakaba Wa Shugaban Hukumar Zaben Kasar Congo Takunkumi
Amurka ta sanar da kakaba takunkomain a kan wasu daga cikin jami'an hukumar zabe ta kasar Congo.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar ad rahoton cewa, a cikin wani bayani da ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta fitar, ta bayyana cewa gwamnatin Amurka ta kakaba takunkumin a kan wasu manyan jami'an hukumar zaben jamhuriyar Dimukradiyyar Congo.
Bayanin ya ce shugaban hukumar zaben kasar Congo da kuam wasu manyan na hannun damarsa suna daga cikin wadanda wanann takunkumi zai shafa, kamar yadda kuma wanann takunkumi zai shafi alkalin alkalan kasar, wanda shi ne ya amince da sakamakon zaben da aka gudanar a kasar, wanda ya jawo cece-ku ce.
Takunkumin dai zai hada da rube dukaknin asusun ajiya da suke da su a Amurka, da kuma hana su shiga cikin kasar ta Amurka.