Najeriya: Akalla Mutane 39 Ne Suka Mutu A Zabukan Ranar Asabar
Cibiyoyi da kungiyoyi masu zaman kansu da suka sanya ido a zaben Najeriya sun ce akalla mutane 39 ne suka rasa rayukansu a lokacin gudanar da zabukan.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kungiyoyi da cibiyoyi kimanin 70 da suka sanya ido a zaben Nijaeriya suka fitar sun tabbatar da cewa, bisa ga bayanan da suka tattara, akalla mutane 39 ne suka rasa rayukansu a lokacin gudanar da zabukan.
Bayanin ya ce kimaninin rumfunan zabe dubu 120 ne a fadin Najeriya, kuma mafi yawansu babu isassun 'yan sanda da suke gudanar da ayyukan tsaro yadda ya kamata, duk kuwa da cewa a wurare da dama ba a samu hatsaniya ba, amma a wasu jahohin da suka hada da Rivers, Bayelsa da Delta, inda a cikin wadannan jahohi mutane 31 suka rasa rayukansu, mutane 8 an kashe su ne a cikin sauran wasu jahohin.
Sai dai a nasu bangaren jami'an 'yan sanda sun ce suna tsare da mutane kimanin 120 wadanda ake zarginsu da laifuka daban-daban a lokacin zaben, ad suka hada kisan mutane, sace akwatunan zabe da sauransu.