Najeriya: Hukumar Zabe Ta Fara Bayyana Sakamakon Zaben Ranar Asabar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35367-najeriya_hukumar_zabe_ta_fara_bayyana_sakamakon_zaben_ranar_asabar
Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya ta fara bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata a yau litinin a Abuja.
(last modified 2019-02-25T11:47:20+00:00 )
Feb 25, 2019 11:47 UTC
  • Najeriya: Hukumar Zabe Ta Fara Bayyana Sakamakon Zaben Ranar Asabar

Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya ta fara bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata a yau litinin a Abuja.

Sakamakon zabe na farko da aka fara bayyanawa shi ne na Jihar Ikiti, inda a zaben shugaban kasa dan takarar jam’iyyar APC  yake gaba da kuri’u 219,231, a yayin da PDP yake bi masa da kuri’u 154,032.

Sai kuma sakamakon zaben Jihar  Osun inda namma jam’iyyar APC ta zo gaba da kuri’u 347,634, sannan jam’iyar PDP ta zo matsayi na biyu da kuri’u 337,377 tare da bambancin kuri’u 10,257.

Sai kuma na babban birnin tarayya Abuja inda Jam’iyyar PDP ta zo ta farko sai kuma jam’iyyar APC ta zo ta biyu.