Najeriya: Atiku Zai Kalubalanci Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Kotu
Dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya Alh. Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Asabar a kotu.
Ya ce dole ne ya yi hakan saboda ceto demokradiyya daga ruhsewa a kasar, inda ya ce bai amince da sakamakon zaben ba, saboda an aikata abubuwa na ba daidai ba da nufin kayar da jam’iyyar adawa ta PDP da karfin tuwo.
Atiku Abubakar ya bayar da misalai da wasu wurare da ya ce an samu hatsaniya, kuma wasu daga cikin wuraren PDP ce take da rinjaye amma mahukunta suka yi gum da bakunansu domin hakan ya cutar da kuri’un da PDP za ta samua wadannan yankuna.
Hukumar zaben Najeriya dai ta fitar da sakamakonta na karshe kan zaben, inda ta tabbatar da cewa shugaba Buhari da ke kan karagar mulki shi ne ya lashe zaben.