MDD: Yan Gudun Hijiran Najeriya A Kamaru Suna Komawa Gida
Majiyar hukuma mai kula day an gudun hijira ta MDD daga birnin Geneva ta bayyana cewa akalla yan gudun hijiran Tarayyar Najeriya a Kamaru 10,000 ne suka koma gida duk tare da cewa akwai sauran barazana na mayakan boko haram su sake kai masu farmaki.
Kamfanin dillancin labaran reuters yan gudun hijira daga garin Rann kimani dubu 40 ne suka shiga kasar Kamaru don gudan hare-heren mayakan boko haram a cikin watan Decemban day a gabata.
Gwamnatin kasar Kamaru ta kori yan gudun hijira kimani 9000 a cikin watan day a gabata, wanda hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Amma daga baya wasu yan gudun hijirar da radin kansu sun ga yakamata su koma gida. Labarin ya kara da cewa a halin yanzu daruruwan yan gudun hijiran Najeriya wadanda suka fito daga garin Rann suna kan hanyarsu ta komawa gida da kafa. Nisan garin Ran da kan.
Kafin hare-haren mayakan boko haram kan garin na Ran a cikin watan Decemban day a gabata, sojojin kasar sun janye daga garin wanda ya bawa mayakan na boko haram wata dammar ta fadawa garin ba tare da mai kare shi ba.