Mambobin Kwamtin Zaman Lafiya Sun Gana da Atiku Abubakar
Mambobin kwamitin tababtar da zaman lafiya kan sha’anin zaben Najeriya karkashin shugabancin tsohon shugaban mulkin soji a najeriya Abdussalami Abubakar sun gana dad an takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.
An gudanar da tatatunawar ne a asirce a gidan Atiku Abubakar da ke unguwar Asokoroacikin birnin Abuja, kuma wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP sun halarci wurin, da suka hada shugaban jam’iyyar na kasa, da kuam shugabannin majalisun dokokin kasar na dattijai da wakilai.
Abdussalmi Abubabakr da ya jagoranci tawagar kwamitin ya bayyana cewa, bababr manufar tattaunawar dai it ace kokarin kaucewa duk wani abin da iya faruwa na rikici bayan zaben, domin kuwa a cewar akwai bababn korafi daga bangaren jam’iyyar PDP dangane da sakamakon zaben.
A daya bangaren kuma Abdussalmi Abubakar tare da tawagar kwamitin sun gana da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajoa kan wannan batu.
Jam’iyyar PDP dai ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa, inda ta ce an tafka magudi maras misiltuwa a wannan zabe, kuma tana da kwararan hujjoji da zata gabatar a gaban kotu a kan hakan.