​Macky Sally a Sake Lashe Zaben Shugaban kasa A Senegal
(last modified Fri, 01 Mar 2019 20:49:07 GMT )
Mar 01, 2019 20:49 UTC
  • ​Macky Sally a Sake Lashe Zaben Shugaban kasa A Senegal

Hukumar zabe mai zaman kanta a Senegal ta fitar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar, tda ke tabbatar da cewa Macky Sall ne ya sake lashe zaben.

Macky Sall ya sake lashe zaben shugabancin kasar ne da sama da kashi 58% na kuri’un da aka kada a ranar lahadin da ta gabata, indaIdrissa Seck ya zo a matsayin na biyu da sama da kashi 20%.

Shugaban hukumar zaben na Senegal Demba Kandji ya ce kashi 66.24 ne na dukkanin mutanen da suka yi rijista suka kada kuri’unsuazaben.

Idriss Seck wanda wannan ne karo na 3 da ya ke tsayawa takarar shugabancin kasar wanda kuma shi en ya zo a matsayi an biyu a zaben, ya ce za su kalubalanci sakamakon zaben a kotu.

Sai tuni bangarori na kasa da kasa da suka hada da kungiyar tarayyar turai tarayyar Afrika, ECOWAS suka yaba da yadda aka gudanar da zaben, tare da bayyana cewa ya gudana cikin tsafta.