Mambobin Kwamitin Zaman Lafiya Sun Gana Da Buhari A Aso Rock
Mambobin Kwamitin zaman lafiya sun shiga ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin tarayya Aso Rock.
Jaridar Vanguard ta Najeriya ta bayar da rahoton cewa, kasa da sa’o’i 24 bayan da suka gana da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, kwamitin zaman lafiya ya shiga ganawa makamanciyar hakan tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. An gudanar da ganawar sirrin ne tare da Buhari a fadar Shugaban kasa da ke Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa an fara ganawar ne da misalin karfe 3:00 na rana a ofishin Shugaban kasa. Wadanda suka halarci ganawar sun hada da tsohon Shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar, babban limamin coci na Sokoto, Hassan Matthew Kukah, da kuma Cardinal John Onaiyekan.
Har ila yau an rawaito cewa shugaban jamíyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ma na wajen. A baya dai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da ya sha kaye a zaben 2019, Atiku Abubakar ya gabbatar da wasu muhimman bukatu 5 da ya ke so daga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari. Tsohon mataimakin shugaban kasar ya gabatar da bukatun ne a yayin ganawarsa da wata tawaga daga kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya).