Zanga-zangar Kyammar Buteflika Na Yaduwa A Aljeriya
(last modified Sat, 02 Mar 2019 14:27:50 GMT )
Mar 02, 2019 14:27 UTC
  • Zanga-zangar Kyammar Buteflika Na Yaduwa A Aljeriya

Dubban mutanen kasar Aljeriya ne su ka gudanar da Zanga-zangar nuna kin amincewa da sake tsayawar takarar shugabanci na Abdulaziz Buteflika.

Zanga-zangar ta jiya Juma’a ita ce mafi girma wacce aka yi a  kasar ta Aljeriya da take yin kira ga shugaba Butaflika da kada ya sake tsayawa takarar shugancin kasar karo na biyar.

Wasu kafafen watsa labaru na kasar ta Aljeriya sun ce mutum guda ya rasa ransa a sanadiyyar taho mu gama da jami’an tsaro.

Wata majiyar tsaron kasar ta kuma tabbatar da cewa ya zuwa yanzu mutane 63 ne su ka jikkata kuma an kame wasu mutanen 45.

Shugaba Butaflika mai shekaru 82 ya dare kan mulkin kasar ne tun a 1999. A shekarar 2013 ya sami shanyewar jiki abinda ya tilasta masa yin jiyya a kasar Faransa.

A yau Asabar  ma an kai shugaban kasar ta Aljeriya asibitin birnin Geneva saboda sake tabarbarewar lafiyarsa.