Najeriya : Fashewar Bututun Mai, Ta Yi Ajalin Mutum Fiye Da 50
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35432-najeriya_fashewar_bututun_mai_ta_yi_ajalin_mutum_fiye_da_50
Fiye da mutane 50 Sun rasa rayukansu sanadiyyar fashewar bututun man fetur a Najeriya.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Mar 03, 2019 04:07 UTC
  • Najeriya : Fashewar Bututun Mai, Ta Yi Ajalin Mutum Fiye Da 50

Fiye da mutane 50 Sun rasa rayukansu sanadiyyar fashewar bututun man fetur a Najeriya.

Kamfanin dillancin labarun Anatoli ya nakalto cewa; Bututun man fetur din ya fashe ne a Jahar Bayelsa da ke kudancin kasar a jiya Asabar.

Kawo ya zuwa yanzu babu wani cikakken bayani akan dalilin fashewar bututun, sai dai wasu jami’an gwamnati a yankin sun zargi matasa da fasa bututun saboda dibar albarkatun mai.

A baya an sha samun irin wannan asarar rayukan saboda fashewar bututun wanda kan faru ta hanyar fasa shi da ake yi.

A watan Oktoba na shekarar 2018, mutane 24 ne su ka kwanta dama saboda fasa bututun da aka yi.

A birnin Ikko ma mutane 150 sun taba mutuwa saboda fashewar bututun a  ranar 12 ga watan Mayu na shekarar 2006.