Masar: An saki Dan Jarida Mahmud Abu Zaid Daga Gidan kaso
Mahukuntan kasar Masar sun saki dan jarida Mahmud Abu Zaid da ake tsare da shia gidan kaso tsawon shekaru biyar da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a yau Litinin an saki Mahmud Abu Zaid wanda aka fi sani da Shaukan, wanda fitaccen dan jarida a kasar Masar da ake tsare da shi.
An dai kama Shaukan ne a ranar 14 ga watan Agustan 2013, a lokacin da jami'an tsaron Masar suka tarwatsa dubban magoya baayan Mohammad Morsi wanda Abdulfattah Sisi ya hambarar ad gwamnatinsa a lokacin.
Jami'an Masar sun kai farmaki tare da yin amfani bindiggi wajen tarwatsa dubban 'yan kungiyar Ikhwanul musulmi da suka tarua dandalin rabi'atul Adwiyyah a tasakjiyar birnin Alkahira, inda suka kashe mutane fiye da 700 daga cikin magoya Muhammad Morsi, kuma bisa hakan ne kame Abu Zaid Shaukan bisa hujjar cewa ya daukl hotuna a lokacion da jami'an tsaro suke kashe mutane a dadndalin rabiat Adwiyyah, bayan da Sisi ya yi wa Morso juyin mulki.