Babbar Kungiyar Malamai Ta Aljeriya Ba Ta Amince Da Takarar Butaflika Ba
Babbar kungiyar malaman addinin mulsunci a kasar Aljeriya ta nuna rashin amincewarta da tsayawar Butaflika takarar shugabancin kasar domin neman wa’adi na biyar.
Shafin yada labarai na Madina news ya bayar da rahoton cewa, a zaman da ta gudanar a jiya, babbar kungiyar malaman addinin muslucni ta kasar Aljeriya ta fitar da bayaninta, inda take yin kira ga shugaba Butaflika da ya hakura da batun neman mulkin kasar a karo na biyar, ya mayar da hankali wajen neman lafiyarsa.
Haka nan kuma kungiyar ta mika kira na musamman ga ‘yan siyasa musamman daga bangaren jam’iyya mai mulki a kasar ta Aljeriya, da su sake yin nazari kan wannan batu, kuma su fifita abin da yake maslaha ga kasa maimakon fifita abin da yake maslaha gare su ko jam’iyyarsu.
Kamar yadda kungiyar ta ce dole ne a saurari jama’a da irin korafinsu, kuma wajibi ne a aiwatar da abin da mafi yawan jama’ar suke bukata.
Duk da irin wadannan kiraye-kiraye da kuma zanga-zangar da ake gunarwa akasar ta Aljeriya, jam’iyya mai mulki a kasar ta sake tsayar da Butaflika amatsayin dan takararta.