Masu Zanga-Zanga A Aljeriya Sun Bukaci Sauyin Gwamnati A Kasar
(last modified Sat, 09 Mar 2019 14:49:43 GMT )
Mar 09, 2019 14:49 UTC
  • Masu Zanga-Zanga A Aljeriya Sun Bukaci Sauyin Gwamnati A Kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Aljeriya APS ya sanar da cewa masu zanga-zanga a babban birnin kasar da ma sauran garuruwa sun bukaci 'sauyin gwamnati' a kasar maimakon kiran da a baya suke yi na samar da 'sauye-sauye na siyasa'.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo kamfanin dillancin labaran na APS yana cewa masu zanga-zanga a bangarori daban-daban na kasar Aljeriyan sun fara sauya bukatar da suke da ita na samar da sauye-sauye na siyasa zuwa ga kiran da a kawar da gwamnatin shugaba Abdelaziz Bouteflika ta kasar.

Cikin 'yan kwanakin nan dai dubun dubatan al'ummar Aljeriyan ne suke ci gaba da gudanar da zanga-zangogi a garuruwa daban-daban na kasar don nuna rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika, dan shekaru 82 na sake tsayawa takarar shugaban kasar duk kuwa da tsananin rashin lafiyar da yake fama da shi.

Masu zanga-zangar dai suna bukatar shugaban ne da ya sauka daga karagar mulkin kasar da ba wa wasu damar ci gaba da shugabancin a zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 18 ga watan Aprilun wannan shekara ta 2019.